1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramta sana'ar Achaba a garin Kaduna

May 21, 2014

Nakasassu da ke Kaduna sun koka game da dokar hana mutane 2 hawa Babur, ko sana'ar Achaba, al'amarin da ya jefa daruruwar mutane cikin mawuyacin hali.

Cotonou Benin
Hoto: Getty Images

Tuni dai hadaddiyar kungiyar Makafi da Kutare da Guragu ta fidda wata takarda kan yadda wannan doka za ta tauye hakkokin Nakasassu masu zirga-zirgan yau da kullun kan baburansu, wanda a kan haka ne suke bukatar gwamnatin da ta gaggauta cire jama'a masu fama da nakasa a wannan dokar bisa la'akari da irin wahalhalun da za su fada, kamar dai yadda tsohon mataimakin shugaban Kungiyar Nakasaassu ta kasa Comrade Rilwanu Abdullahi mohammed ke cewa;

" Mu guragu, mu ne wadanda wannan cuta tafi illa a kanmu domin, bamu da kafafuwa da kuma sauran ababan da muke ganin za mu iya motsa jikin mu wajan kai-da-komowa a harkokin mu na yau da kullun da muke gudanarwa, kaddamar da wannan dokar tamkar, an kara nakasa dubban nakasassu ne bisa la'akari da irin munanan wahalhalun da za mu fada ciki, a saboda haka ne muke kira ga gwamnati da ta gaggauta cire nakasassu a cikin dokar hana hawa babura da ta kakabawa alummanta".

Kiraye-kirayen kungiyoyin jama'a da ke fama da nakasa dai a nan ita ce na wajen tabbatar da ganin gwamnatin ta tsame Nakasassu da ke anfani da babura mai kafa 3 na daukar Guragu, da kuma yadda Makafi za su sami masu daukar su zuwa dukkanin wuraren da su ke bukatar zuwa.

Bugu da kari hatta Kutare da sauran jama'a masu fama da bugun jannu sun nunar da cewa suna bukatar keke- napef dan daukar su zuwa koina, amma gwamnatin ba ta wadata su da shi ba a cewar Kwamrade Muntari Sale kakakin kungiyar makafin arewa:

"Wannan doka za ta jefa al'ummanmu cikin mawuyacin halin rayuwa, domin babban matsalar da makaho ke fuskata ita ce na rashin gani,saboda haka muna matukar fatan ganin cewa, gwamnatin ta yi dukkanin abu mai yiwuwa wajan ceto rayukan mu jama'a masu fama da nakasa".

'Yan AchabaHoto: AP

Ita dai gwamnatin jahar kaduna ta sanya wannan dokar ne saboda yadda korarrun 'yan Achabar daga wasu jihohi suka yi mata kakagida kamar dai yadda diraktan watsa labarai na fadar gwamnatin jahar kadunan Ahmed maiyaki ke cewa;

"dukkanin korarrun 'yan Achaba da aka koro su daga wasu jihohin arewa, anan Kaduna ne suka yada zango, kuma basa kulawa da lafiyar jikinsu da kuma yadda ake yin anfani da babura wajan kai farmaki da sauran ayyukan da basu dace ba".

Comrade Mohammed Auwal shi ne shugaban kungiyar masu baburan haya a kaduna: " ya kamata gwamnati ta sani da cewa akwai kimanin miliyan daya da dubu dari 6 da 50 na mutane masu aikin baburu da aka yi masu regista, amma gwamnatin ta kawo baburu na mutane guda 700, hakan bai da ce ba, muna bukatar karin baburan hawa don taimakawa alumman".


Diractan watsa labarai na fadar gwamnatin jahar kaduna cewa ya yi maimakon su tsaya tayar da jijiyoyin wuya, kamata yayi su rubuta tare da sanya hutunan irin baburan da suke hawa don tattaunawa game da nazarin yadda za a warware matsalar Nakasassu.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar