1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hare-harbe sun halaka mutane 13 a Afirka ta Kudu

Suleiman Babayo LMJ
June 10, 2026

Harbe-harbe sun halaka mutane 12 a daya daga cikin manyan biranen Afirka ta Kudu.

Jami'an tsaron Afirka ta Kudu
Jami'an tsaron Afirka ta KuduHoto: Shiraaz Mohamed/Xinhua/picture alliance

A wannan Laraba, harbe-harben 'yan bindiga dadi sun halaka mutane 12 cikin unguwar 'yan rabbana ka-wadatamu na birnin , daya daga cikin manyan biranen kasar Afirka ta Kudu.

Laifuka na ta'azzara

Akwai kimanin 'yan bindiga guda 10 lokacin da aka samu harbe-harben.

Jami'an tsaron Afirka ta KuduHoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

'Yan sanda suna ci gaba da binciken dalilan wannan harbe-harbe, inda kasar ta Afirka ta Kudu take ganin matsalolin masu amfani da makamai wajen kawo tashe-tashen hankula, musamman wadanda ake dangantawa da hakar ma'adanai a kasar.

Afirka ta Kudu ta kasance kasa mafi ingancin tattalin arziki na zamani tsakanin kasashen Afirka, amma tana fama da matsalolin aikata miyagun laifuka musamman tsakanin matasa masu zaman kashe wando.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW