Hare-hare a Brussels
March 22, 2016 Hukumomin kasashen Turai sun kara tsaurara matakan tsaro a filayen tashi da saukar jiragen sama da tintunan kasashen, su bayan wani mumunan hari da aka kai a filin tashin jiragen saman Brussels da tashar jiragen kasa.
Kawo lokacin rubuta wannan labarin, a kalla mutane 34 suka mutu a yayin da wasu 170 suka sami raunuka, sakamakon harin kunar bakin wake da ya shafi zauren tashin fansinjojin filin jirgin sama da kuma wani harin da aka kai a tashar jiragen karkashin kasa duk dai a birnin na Brussels a safiyar yau.
Hukumomin gudanarwar filin jirgin saman birnin Brussels suka ce tuni aka fara gudanar da bincike, a yayin da kasashen Britaniya da Portugal suka kira wani taron gaggawa bayan daukar matakan tsaro a filayen jiragen saman kasashensu.
Kazalika mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida kasar Ostiriya, Karl-Heinz Grundboeck, shi ma ya ce tuni kasar ta baza 'yan sanda a kan titunan filayen jirgin sama da tashoshin jiragen kasa a Vienna babban birnin kasar gami da wasu manyan biranen kasar.
Suma hukumomi a kasar Jamus sun dauki irin wadannan matakan domin kare lafiya da dukiyoyin jama'a.