1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-hare a Irak

June 20, 2007

Ƙawancen rundunar Amurika da ta sojojin Irak sun ƙaddamar da wani babban tsari na kai farmaki a yankin Diyala, da su ka ɗauka tamkar maɓuyar mayaƙan Alƙa´ida.

Dubbunan sojojin Amurika sun bazu a wannan yanki ,inda su ka yi ta dura mikiya, a gidaje da unguwani, wanda a sakamakon hakan, mutane fiye da 30 su ka rasa rayuka a yau laraba.

Shugaban rundunar Amurika a Irak, Jannar Mick Bednarck, ya ce wannan hari tamkar somin taɓi, ne, wato za su ci gaba har sai sun kakkaɓe wannan yanki daga barazanar ƙungiyar Alƙa´ida.

Irin wannan hari ya wakana a yankunan Baƙuba, Fallujah Mossul da Nasiyah.

A daidai lokacin da ƙasar Irakin ke fama da hare-hare babu kaƙƙabtawa, shugaban ƙasa Jalal Talabani ya fara ziyara aiki a birnin Pekin na ƙasar Sin, inda zai roƙi hukumomin Sin, su yafe bassusukan da su ka tambayo ƙasar sa