Hare hare a jihohin Gombe da Kano a Najeriya
February 25, 2012An ba da rahoton cewar wasu 'yan bindiga sun kai wasu jerin munanan hare-hare a Gombe fadar gwamnatin Jihar da ke a yankin arewa maso gabashin Tarrayar Najeriya. An dai shafe sa'o'i da dama a daran jiya ana jin ƙarar fashewar abubuwan da kuma harbe-harben bindigogi abinda ya tilassawa mazauna birnin shige wa gidajen su.Tun daga misalin karfe bakwai da rabi na yammacin jiya ne aka fara jin tashin Bama-bama da kuma ƙarar bindigogi inda aka raba dare ana jin musayar wuta babu ƙaƙƙautawa.Hayaƙi ya turniƙe sama inda aka shaida ganin wuta na ci a babban Ofishin ‘yan sanda dake Gombe wanda kuma yake kusa da tudun hatsi da ke tsakiyar birnin.
Haka kuma rahotannin sun nuna cewa an kai hari a gidan yari sai dai babu cikakken bayani na irin ɓarna da aka yi a dukkanin wuraren.kawo yanzu.wakilin dw a Gombe ya ce har a safiyar yau an ci gaba da yin harbe harbe.Wannan dai shi ne karo na farko da al-ummar Gombe ke tsintar kan su a irin wannan munanan Hare-Hare .Gwamnatin jihar ta bakin Sakataren ta Abubakar Suke Bage ta sanar da dokar hana fita na tsawon awowi 24 har sai abinda hali ya yi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita .Mohammed Nasiru Awal