Hare-hare a kan wani asibiti a Libiya
June 12, 2016Talla
Majiyoyin tsaro sun ce harin ya yi kaca-kace da asibitin tare da haddasa asara mai yawan gaske.Sojojin masu yaki da Kungiyar IS wadanda galibinsu 'yan asilin garin Misirata ne da ke a yankin yammancin Libiyar na kalubalantar masu kai harin kunar bakin wake na Kungiyar IS.
Kuma kawo yanzu an kashe 120 daga cikin sojojin yayin da wasu 500 suka jikkata. a sumamen da Kungiyar IS ta ke kai musu ba dare ba rana.