SiyasaAfirka
Lamuran tsaron Burkina Faso sun sukurkuce
August 20, 2021Talla
Ana tsoron mutanen da suka mutu sun kai 100 a hare-hare tsageru masu nasaba da jihadi a kasar Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka. Hukumomin tsaron sun bayyana halaka 'yan ta'addan fiye da 80, kuma rikicin ya raba fiye da mutane 400 da gidajensu kusa da iyakar kasar ta Burkina Faso da Mali.
Hare-hare masu matsanancin ra'ayin Islama na ci gaba kassara kasar ta Burkina Faso wadda ke sahun gaba a kasashe 'yan rabbana ka wadata mu, lamarin da ya shafi galibin kasashen yankin Sahel.