An kashe gomman fararen hula a Sudan
March 8, 2026
Talla
An kai jerin hare-haren ne kan kasuwannin Abu Zahad da kuma Wad Banda da ke yammacin Kordofan, yanki mai arzikin albarkatun kasa a Sudan, wanda a halin yanzu shi ne filin daga mafi muni a yakin kusan shekaru uku da ake gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF.
Karin bayani: Sudan: Kuncin rayuwa ta yi tsanani
Wani likita da ke asibitin Abu Zabad ya ce an samu rahotannin jikkatar mutum 59. Tuni aka fara dora alhakin harin kan dakarun kasar, sai dai kuma rundunar sojin Sudan ta musanta zargin, inda ta ce dakarunta ba su kai hari kan yankunan fararen hula. Tun bayan barkewar yaki a Sudan a watan Afrilun shekarar 2023, ana zargin bangarorin da ke fada da juna da aikata laifukan yaki a yankunan fararen hula.