Hare-hare na ta'addanci a Kabul
February 1, 2016Talla
Masu aiko da rahotonnin sun ce mutumin ya tayar da bam ɗin da ke a jikinsa a sa'ilin da ya isa a wajen wani taron jama'ar da suka ja dogon layi a bakin wani oifishin 'yan sanda da ke yammacin birnin
Tuni da Ƙungiyar Taliban ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin kai harin.Kuma Yanzu haka ministan cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere na yin ziyara a birnin na Kabul.Inda zai tattauna da hukumomin ƙasar a kan buƙatar dakatar da yawan kwararan 'yan gudn hijira daga Afganistan ɗin zuwa Jamus.