Hare-haren ƙunar baƙin wake a Irak
July 17, 2006Talla
A ci gaba da hare haren ƙunar baƙin wake a ƙasar Iraki, mutane kussan 50 su ka rasa rayuka, wasu kuma fiye da 40 su ka ji raunuka,daga assubahin yau, zuwa yanzu.
Mace macen na yau, sun abku, a a sakamakon harin da wasu mutane ɗauke da makamai su ka kai, cikin kasuwar Mahmudiyah, da ke tazara kilomita 30 a kudancin Bagadaza.
Birnin Muhamadiyah na cikin yankin da a ka raɗawa suna zirin mutuwa, ta la´akari da haren haren da ya ke fuskanta lokaci, zuwa lokaci.