Hare-haren Amirka ta sama na tasiri kan kungiyar IS
October 8, 2014Hare-hare ta sama da Amirka ke jagoranta sun yi nasarar tura mayakan Siriya baya zuwa garin Kobane, garin Kurdawan Siriya da ke kan iyaka, wanda da suka yi niyyar mamayewa bayan da suka yi makonni uku suna kai hari, kamr dai yadda jami'an Kurdawa suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters.
Wannan gari dai na daukar hankalin al'ummar kasa da kasa tun bayan da kungiyar ta IS ta koro akalla mutane dubu 180 daga mafi yawan yankunan Kurdawa, abinda ya tilasta musu zuwa Turkiyya, abinda ya fusata Kurdawan Turkiyyan har su ma suka fara sanya baki.
Daga farkon wannan makon ne kungiyar IS ta sanya tutarta daga yankin gabashin kasar kuma tun daga wannan lokacin ne Amirka tare da tallafin kasashen larabawa na yankin Gulf, da ke adawa da akidun kungiyar ta IS suka ribanya hare-harenta ta sama