1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare haren bama-bamai a majami'un Kenya

July 1, 2012

Mutane da dama sun rasa rayukansu a wasu majami'u biyu na kasar Kenya sakamakon wasu hare-haren bama-bamai da 'yan bindiga suka kaddamar a wannan lahadin.

A fire burns in a clothing stall after an explosion in a shopping complex in Kenya's capital Nairobi, May 28, 2012. A blast struck a shopping complex in Nairobi's business district during Monday's lunch hour, wounding more than a dozen people, but it was not immediately clear what had caused the explosion. Dense black smoke billowed from the badly damaged building and sirens blared as emergency service crews rushed to Moi Avenue, a major road running through the city centre. REUTERS/Johnson Mugo (KENYA - Tags: SOCIETY CIVIL UNREST CRIME LAW)
Anschlag in NairobiHoto: Reuters

Wasu tagwayen hare haren bama-bamai da aka kaddamar a majami'u biyu na wani gari da ke arewacin Kenya sun haddasa asarar rayukan mutane 16 tare da jikata wasu da dama. Bisa ga bayanan da rundunar 'yan sandan kasar ta bayar dai, wasu 'yan bindiga da suke rufe fiskokinsu ne suka harba bama-bama a cocuna biyun na garin Garissa tare da bude wuta akan kiristoci da ke ibada a cikinsu.

Wadannan dai su ne hare hare mafi muni da Kenya ta fiskanta tun bayan da sojojinta suka fara sa in sa da kungiyar al-shabab a karshen shekara ta 2011. Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin wadannan hare haren. Sai dai gwamnatin Kenya na alakantasu da al-shabab ta Somaliya da ke ta tsattsauran ra'ayin islama.

kungiyar musulmin kenya ta yi tir da wannan danyen aiki da ke neman zaman ruwan dare a kasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Usman Shehu Usman