Hare-haren bama-bamai a Somaliya
September 7, 2013Talla
Majiyoyin jami'an tsaro sun ce, an kai harin ƙunar baƙin waken ne, a kan wani gidan cin abinci da ke kusa da wani babban zauren gudanar da taruka, wanda jama'a ke yawan zuwa can. Wani babban jami'in 'yan sanda ya ce da farko wata motar ce ɗauke da bama-bamai ta fashe a bakin gidan cin abincin.
Sannan ya ce a lokacin da jama'a suka fara yin dandazo a wurin da lamarin ya faru, wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da jigidar bam ɗin da ke a jikinsa. Zauren na yin tarukan na Mogadishu wanda a ka buɗe a bara, bayan da ya kasance a rufe kusan shekaru 20, sau biyu a wannan shekara 'yan ƙungiyar Al-Shebab na kai hare-hare a kansa.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh