Hare-haren Boko Haram na karuwa a jihar Diffa
October 21, 2015 A hannu daya kuma mayakan na Boko Haram sun kai wani harin a Assaga da ke da nisan kilometa tawas da birnin na Diffa, sai dai rahotanni na cewa sojojin na Nijar sun hallaka maharan masu yawan gaske inda wasu ma daga cikinsu suka buya cikin garin abun da ya sanya sojojin suka dauki mataki hana shiga da futa cikin garin domin zakulosu. Hare-haren dai sun faru ne cikin dare inda mazauna birnin Diffa suka ce sun ji tashin hankalin da ya saka su cikin fargaba yayin da suka yi ta jin karan wasu manyan ababe na fashewa.
Wadan an hare-haren kunar bakin waken da 'yan kungiyar ta boko haram
suka haukata aikatawa a yankin na Diffa, sun zo ne a dai dai lokacin da sabon gwamnan jihar ta Diffa Janar Abdou Kaza ya isa birnin na Diffa a ranar Talata. To amma kuma jama'a na fasara yawan kai hare-haren ne da janyewar sojojin kawance na kasashen Tafkin Chadi daga garuruwan Damassak da Malamfateri na Tarayyar Najeriya, wanda ake ganin hakan ya haifar da yawaitar hare-haren yan kungiyar a kasar ta Nijar tare kuma da hallaka rayuka barkatai sakamakon dauki dai-dai lokaci zuwa lokaci a yankin.