Ana ci gaba da fuskantar hare-haren Boko Haram
December 5, 2018Daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu bayan da mayakan Boko Haram suka kai hari a garin Gudunbali da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno a ranar Talata da dare inda aka dauki lokaci ana fafatawa da jami'an tsaron Najeriya.
Mayakan na Boko Haram sun afka wa garin na Gudunbali inda suka bude wuta na kan mai uwa da wabi abin da ya sa mazauna garin suka tsere.
Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani na barnar da harin ya haifar wanda mutanen da suka gudu daga garin suka ce an dauki tsawon lokaci ana musayar wuta tsakanin bangaren mayakan Boko hHram da sojojin Najeriya a bangaren daya.
Mayakan na Boko Haram da sojojin Najeriya sun kuma fafata a garin Malumfatori a ranar Litinin da dare, sai dai har ya zuwa wannan lokaci babu wani bayanin da bangaren jami'an tsaro suka bayar kan wannan hari.
To sai dai wasu bayanai da ba na hukumomi ba sun an hallaka soja guda daya tare da jikkata wasu da dama.
Yanzu haka dai hankulan al'ummomin jihohin Borno da Yobe sun tashi matuka ganin yadda mayakan ke kai hare-hare ba kakkautawa a sansanonin sojoji da kuma garuruwa a kusan kullum yanayin da ke kama da wanda aka shiga a shekarun 2014 zuwa 2015.
Malam Isyaku Adamu wani mazaunin Maiduguri ya shaida cewa sun kasa fahimtar abin da ke faruwa a wannan lokaci bayan samun saukin hare-haren a a baya.
A cewar Ibrahim Mustapha sun yi zaton zuwan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jihar Borno za a samu sauki wadannan hare-haren amma kullum abin karuwa yake yi.
Sabbin hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Najeriya suka sanar da cewa mayakan Boko Haram sun hallaka sojoji takwas tare da kona wata tankar yaki a wani hari da suka kai a Buni Gari da ke jihar Yobe.
Karuwar wadannan hare-hare a wannan lokaci ya sa shugabannin addini da na al'umma kamar Khalifa Sharif Ali Shekh Abul Fathi yin kira ga shugabannin da su tashi tsaye su sauke hakkin da ya rataya a wuyansu.
Kokarin jin ta bakin jami'an tsaro dai ya ci tura, inda kuma ya zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wata sanarwa da jami'an tsaro suka bayar kan sabbin hare-haren da kuma matakai da suke dauka na magance su.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta bukaci manyan hafsoshin sojojin kasa da da na sama da su koma da zama a shiyyar Arewa maso Gabacin kasar har sai al'amuran tsaro sun inganta, lamarin da masana da masharhanta ke ganin ba zai haifar da komai ba, tun da ba karo na farko kenan da gwamnatin ke ba da irin wannan umurni ba.