1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hare-haren Boko Haram kan sojojin Najeriya

April 10, 2026

Sojojin Najeriya sun tabbatar da mutuwar Birgediya Janar O.O. Braimah da wasu sojoji da dama sakamakon hari da mayakan Boko Haram da ISWAP suka kai kan sansanonin sojoji a Benisheikh da Ngamdu da Pulka a Jihar Borno.

Sojojin Najeriya
Sojojin NajeriyaHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Wannan Lamarin ya jefa al'umma cikin rudani a jihohin Borno da Yobe, yayin da mayakan ke kara zafafa hare-hare musamman kan sansanonin sojoji, tare da kashe manyan kwamandojin yaki.

Halin da ake ciki

Sojojin NajeriyaHoto: Audu Marte/AFP/Getty Images

Ciki dai ya duri ruwa inda hanta kada saboda yadda al'ummar jihohin Borno da Yobe suka shaida ganin tashin hankali na tsararren hare-hare da mayakan Boko Haram da ISWAP suka kai a wasu sansaonin Sojojin a jihar Borno.

Hankluan al'ummaya kara tashi bayan da rundunar sojoji ta gaggauta sanar da mutuwar Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah daya daga cikin jajirtattun Sojoji da ke yaki da ta'addanci gami da wasu sojojin da ba a fayyace yawansu ba.

Tuni dai Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya sanar da yin ta'aziyya ga iyalan wannan janar na soja tare da sauran sojoji da suka riga mu gidan gaskiya.

Martanin mutane

Jami'an tsaron NajeriyaHoto: Ahmed Kingimi/REUTERS

A cewar al'ummomin wannan yankin hare-haren na baya-bayan nan abun tashin hankali ne inda da dama ke cewa irin wannan lamari na nuna cewa matsalar tsaro har yanzu tana da girma duk da kokarin da hukumomi ke yi.

Malam Hussaini Garba Sawaba wani mazaunin Maiduguri ne da ke nuna damuwa kan halin da ake ciki dangane da wannan sabbin hare-hare. Shi kuma Malam Muhammad Kamilu cewa babban tashin hankalin shi ne wadanda suke tare musu hare-hare yau su ake kashewa.

Yanzu haka a cikin watanni biyu da suka gabata, an rasa wasu manyan kwamandojin yaki guda uku, baya ga wani Manjo Janar da aka kashe a karshen shekarar da ta gabata, abin da ke nuna yadda hare-haren ke kara tsananta duk da matakan tsaro.

Martanin masana tsaro

Matsalolin tsaron NajeriyaHoto: Deborah Peter/International Rescue Committee/AP Photo/picture alliance

Masana tsaro kamar Manjo Muhammad Bashir Shu'aibu Galma mai ritaya na cewa ya zama dole a sake fasalin harkokin leken asiri da sarrafa bayanai sirri kafin a iya magance wannnan matsala na karuwar karfin mayakan Boko Haram.

Yayin da wasu ke alakanta wannan zafafan hare-hare da shigowar lokacin siyasa, karamin ministan tsaro Alhaji Muhammad Bello Matawalle ya ce ba haka abun ya ke ba, wasu ne ke neman ruruta wannan rikici tare da alakanta shi da siyasa.

Kokarin ji daga bangaren sojojin don samun karin bayanai ya ci tura a lokacin da kura ta lafa a wuraren da aka kai hare-haren inda jama'a suka fara komawa harkokinsu na yau da kullum.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani