Hare-haren Rasha sun kashe mutane da dama a Odessa
December 20, 2025
Talla
Rahotanni daga Ukraine sun yi nuni da cewa akalla mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu 27 suka jikkata a wani harin da Rasha ta kai a cikin dare a birnin Odessa. A sakon da ma'aikatar tsaron Ukraine ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce harin ya rutsa da wata motar bas dauke da fasinjoji a birnin mai tasoshin jiragen ruwa, yayin da wasu motocin dakon kaya da kananan motoci suka kama da wuta a wajen aje su.
Karin bayani: Rasha ta kai munanan hare-hare a kudancin Ukraine
A share guda kuma, dakarun Ukraine sun kai hare-haren jirage marasa matuka kan wani jirgin ruwa na yakin Rasha, da wasu gine-gine a cewar wani kwamdan sojin Kyiv. A cewarsa, jirgin na kai kawo ne a taken Caspian a kuda da wata cibiyar mai d Iskar gas.