Hare-haren t'addanci a Somaliya
April 13, 2016Talla
Mutane sun mutu ne a cikin wasu hare-hare da wasu 'yan bindiga suka kai a kan wata kasuwa da ta saba cika maƙil da jama'a:
Wani babban jami'in tsaro ya ce 'yan bindigar sun jefa gurneti ne a cikin kasuwar da ke a garin Afgoye da ke da nisan kilomita 30 daga Mogadishu babban birnin ƙasar.Ko da shi ke ya zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin amma dai masu aiko da rahotanni na danganta harin da Kuniyar Al-Shebaab.