Hare-haren Ukraine sun karu a kasar Rasha
August 11, 2023Rundunar sojojin Rasha ta sanar da cewa ta lalata wani jirgi marasa matuki mallakin Ukraine a yammacin birnin Moscow, lamarin da ke tabbatar da karuwar hare-haren da ake kaiwa babban birnin kasar. Cikin wani sako da ta wallafa a kafar sadarwa ta Telegram, ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta yi amfani da na'ura mai kwakwalwa wajen kakkabo wannan jirgi da ya fada wani daji ba tare da haddasa asarar rayuka ba.
Sai dai wasu filayen jiragen saman kasar sun dakatar da ayyukansu na wani dan lokaci a matsayin kandagarki kafin komai ya daidaita. Wannan dai shi ne karo na uku a ciki mako guda da ake harbo jirage marasa matuka a birnin Moscow. Ko da a karshen watan Yuli da farkon watan Agusta, an harbo jirage marasa matuka a yankin da ake hada-hadar kasuwanci a Moscow, lamarin da ya barnata wasu sassa na gibe-gine guda biyu.