1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hare-Haren 'yan Boko Haram A Najeriya

June 28, 2011

Ƙungiyar nan ta Boko Haram sai ci gaba da kari hari take yi, lamarin da kan rutsa da farar hula kuma a sakamakon haka ƙungiyar neman afuwa ta ƙasa da kasa tayi kira gare ta da ta dakatar da wannan kashe-kashe na ba gaira

Harin 'yan Boko Haram a MaiduguriHoto: AP

Bayan harin bam da ta kai a shelkwatar 'yan sanda a birnin tarayya na Abuja, misalin makonni biyu da suka wuce, ƙungiyar Boko Haram ta sake kai wasu sabbin hare-haren a birnin Maiduguri, inda mutane da dama suka yi asarar rayukansu. A baya-bayan nan dai ƙungiyar ta sha nanata shirinta na ƙara ƙarfafa hare-harenta kan kafofin gwamnatin Najeriya, sannan a ɗaya hannun kuma ana ƙara samun shaidar dake tabbatar da cewar ƙungiyar na aiki ne hannu-da-hannu da ƙungiyar 'yan ta'adda ta Al-Ƙa'ida.

Bisa ga dukkannin alamu dai ƙungiyar mai zazzafan ra'ayi da aka fi saninta da sunan:"Boko Haram", a shekara ta 2002 ne aka kafa ta a yankin arewa-maso-gabashin Najeriya. Da farkon fari dai, shugabanta Mohammed Yusuf ya kan gabatar da huɗuba da kuma wa'azinsa ne a cikin lumana domin adawa da tasirin al'adun ƙasashen yammaci akan al'umar Musulmi ta arewacin Najeriya. Akasarin magoya-bayansa kuwa matasa ne dake fama da takaici, saboda an yaye su daga makarantu, amma ba su samu guraben aiki ba, kamar dai yadda aka ji daga Solomon Dalung, masharhanci kuma masanin al'amuran shari'a:

"Duk wanda ke neman zama memba a ƙungiyar "Boko Haram" wajibi ne ya miƙa taradunsa na shaidar kammala makaranta domin a ƙone ta. Wato ke nan ƙungiyar ta Boko Haram, ba wani gungu ne na jahilai da ba su san ko binhin ba."

Harin sojoji akan shelkwatar 'yan Boko Haram a Maiduguri a 2009Hoto: picture-alliance/ dpa

Wannan aƙidar tasu ta ƙyamar duk wani ci gaba na zamani da suke ganin bai dace da addinin musulunci ba tayi daidai da irin shigenta da aka fuskanta a arewacin Najeriyar a shekarun 1970 da farkon 1980 a ƙarƙashin taken:"Maitatsine", wadda ta sha fafatawa da 'yan sanda da sojoji. Sai dai kuma ita ƙungiyar Boko Haram kamar yadda akasarin manazarta suke gani, wata manufa ce ta mayar da martani akan mawuyacin hali na rashin adalcin da ake fama da shi a zamantakewar al'uma da kuma matsalar cin hanci da tayi wa 'yan siyasa katutu a Najeriya. Arangama ta farko tsakanin ƙungiyar da jami'an tsaro ta wanzu ne a Maiduguri a shekara ta 2009, wadda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan-Adam suka ce ta haddasa salwantar rayukan mutane kimanin ɗari takwas. Shi kansa shugaban ƙungiyar Mohammed Yusuf an halaka shi, bayan da sojoji suka cafke shi suka kuma danƙa shi a hannun 'yan sanda. Wannan kisan gillar ba shakka na daga cikin abin da ya ƙara ƙarfafa ƙiyayya akan jami'an tsaro da 'yan siyasa a zukatan 'ya'yan ƙungiyar. Dukkan wakilai da masu magana da yawun musulmi da kirista a Najeriya da ma ƙungiyoyin farar hula da 'yan siyasa, na yin kiran neman bakin zaren warware rikicin a cikin lumana. A baya ga shugaba Goodluck Jonathan, shi ma sabon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayi wa ƙungiyar tayin shiga zauren tattaunawa:

Sabon gwamnan jihar Borno Kashim ShettimaHoto: DW

"Matsalar Boko Haram matsala ce ta siyasa kuma a saboda haka ya kamata a shawo kanta a siyasance. Idan muka ce zamu duƙufa akan matakai na soja to kuwa zamu shiga wata gwagwarmaya ce da ba zata tsinana kome ba. Sai dai kuma wajibi ne mu ƙarfafa matsayinmu a duk shawarwarin da zamu yi tare da su."

A dai halin da ake ciki yanzu masu magana da yawun ƙungiyar ta Boko Haram na iƙirarin samu horo daga ƙungiyar Al-Shabab ta Somaliya dake da nasaba da Al-ƙa'ida kuma da yawa daga manazarta a Najeriya sun gaskata hakan. Bugu da ƙari ma dai a 'yan shekarun baya-bayan nan ƙungiyar ta samu ƙarin magoya-baya tsakanin matasan da ba su gamsu da makomar rayuwarsu a arewacin Najeriya ba.

Mawallafi: Thomas Mösch/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani