Hare-haren yan taliban a Afghanistan
March 17, 2007Talla
Mayaƙan taliban a ƙasar Afghanistan, na ci gabada kai hare- hare ,ga rundunar ƙasa da ƙasa ta NATO.
A yau wani hari da su ka abkawa rundunar, ya hadasa mutuwar wani matsahi a yankin Khandar.
Sannan ƙarin mutane 2, da su ka haɗa da soja 1, su ka ji mummunan raunuka.
Shugaban rundunar shiga tsakani ta NATO, a wata sanarwar da ya bayyana ya yi Allah wadai, da wannan hare-haren, wanda ya ce ke hadasa mutuwar fara hulla da basu san hawa ba, balle sauka.
Janar Ton Van Loon, ya yi kira ga al´ummar Afghanistan ta bada haɗin kai, domin tabbatar da tsaro a wannan ƙasa da ke fama da yaƙe-yaƙe.