An halaka mutane 50 iyaka da Chadi
May 24, 2019![Zentralafrikanische Republik UN-Sicherheitstruppen in Bangui](https://static.dw.com/image/18477463_800.webp)
Talla
Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar bayan Allah wadarai da harin sun ce an baza ma'aikatan majalisar a wurin da lamarin ya faru.
Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi gargadi ga kungiyar 3R mai dauke da makamai inda ta bukaci ta mika wadanda ke da hannu wajen harin da ya halaka mutanen.
Mai magana da yawun gwamnati Ange-Maxime Kazagui ya ce bayan wani hari da aka kashe wa kungiyar mutum guda ta rika kai hare-hare na ramuwar gayya. Ana dai zargin mayakan sakan da rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla da shugabanni ciki kuwa har da yarjejeniyar da aka yi a watan Fabrairu.