1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Hari a kan jirgin kasa ya fusata 'yan Najeriya

October 22, 2021

A Najeriya, jama’ar jihar Kaduna da kewaye na nuna damuwa a game da harin da wasu mahara suka kai wa jirgin kasa da ke zirga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja a ranar Laraba.

Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna
Hoto: DW/U. Musa

Wannan harin da ya auku a tsakanin garin Rujana da Dutse da ke a wani yankin kudancin Kaduna al‘amari ne da ya jefa dubban matafiya da ke bin hanyar sake fadawa cikin rashin kwanciyar hankali da kuma rashin sanin makomar yanayin da za su fada ciki a duk lokaci da suka kama hanyar sanadiyyar hare haren ‘yan bindigar daji da suka dade suna ta kokarin tabbatar da ganin cewa sun kai wa wannan jirgi hari.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwa matafiya da tashar DW ta zanta da su, suna cewa lallai dai kam akwai bukatar kara matsa kaimi wajen kaddamar da yaki gadan-gadan a kan ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda da suke addabar matafiya akai-akai a kan wannan hanyar.

Baya ga buda wa jirgin wuta da maharan suka yi, sun kuma lalata hanyar da jiragen na kasa ke bi.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da ake kai wa jirgin kasan hari, domin kowa ko a baya ma, akwai rahotanni da dama da ke nuni da cewa wasu mahara sun kai wa jirgin Kaduna zuwa Abuja hari daidai lokacin da yake daf da shiga Kaduna daga Abuja.

Malam Babangida Kakaki, dan Jarida da ya saba bin hanyar domin zuwa Abuja gudanar da aikinsa, ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan abun takaici.

Ita ma Faiza Mohammed, wata matashiya ce da ita ma ta saba bin jirgin daga Kaduna, ta koka a kan yadda tabarbarewar tsaro yake a yankin arewa, musanmman ma dai tsakanin Kaduna da wasu jihohin shiyyar.

A ranar 27 ga watan Junin 2016 ne dai aka bude zirga-zirgar jiragen kasa a tsakanin Kaduna da Abuja a Najeriyar.