1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe mutane a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
February 4, 2023

A Jamhuriyar Nijar wasu mayakan da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne suk kai mummunan harin ta'addancin da ya halaka 'yan gudun hijira a yankin Tahoua iyaka da Mali

Symbolbild- Nigera - Militärübung
Hoto: Reuters/A. Ross

Wani harin ta'addanci a sansanin 'yan gudun hijirar Mali da ke samun mafaka a yankin Tahoua na Jamhuriyar Nijar, ya halaka mutane tara da raunata mutun daya, kana wasu shida sun yi batan dabo.

Wakilin al'umma a yankin Tillia mai makwabtaka da Mali, yankin da aka kai harin, ya tabbatar da cewa maharan sun far wa sansanin 'yan gudun hijitrar ne kan babura dauke da manyan makamai.

Tsakiyar watan Maris na shekarar 2021, mahara masu alaka da al-Qua'ida sun kai harin kan mai uwa da wabi a wasu garuruwan da ke zagaye da yankin Tillia mai makwabtaka da Mali, inda suka halaka mutane fiye da 100.