Hari a Somaliya ya kashe mutane sha huɗu
September 20, 2012Harin na Mogadishun wanda aka kai shi a Alhamis ɗin nan ya yi sanadiyyar rasuwar mutane goma sha huɗu kamar yadda babban jami'in rundunar 'yan sandan birnin na Moghadishu Kanar Mohammed Dahair ya shaidawa manema labarai, sai dai ya ce kawo wannan lokacin ba su tantance ko mutane nawa ne su ka jikkata ba.
A tasa zantawar da manema labarai, Abdiwali Hassan da ke zaman ɗaya daga cikin jami'an 'yan sandan na Mogadishu ya ce daga cikin waɗanda su ka rasu har da wasu 'yan jaridu guda uku sai dai bai tantance ko harin ya haɗa da manyan 'yan siyasar ƙasar ba.
Tuni dai aka fara zargin ƙungiyar nan ta al-Shabab da ke gwagwarmaya da makamai da alhakin kai hari, sai dai kawo yanzu ƙungiyar ba ta ce uffan ba.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Usman Shehu Usman