1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari akan sojojin NATO a Afghanistan

June 20, 2012

Kungiyar Alqa'ida ta dauki alhakin harin da aka kaiwa dakarun kungiyar NATO a kasar Afghanistan. Mutane 11 suka rasa rayukansu yayin da dama suka jikata.

In this Monday, Sept. 19, 2011 photo, a German soldier rests during a break while on long term patrol near Char Darah, outside Kunduz, Afghanistan. As the U.S. and NATO mark 10 years of war in Afghanistan, a grim picture emerges from scores of interviews over six months across the country with ordinary Afghans, government officials, soldiers, and former and current Taliban. (ddp images/AP Photo/Anja Niedringhaus)
Hoto: AP

Wani harin kunar bakin waken da aka kaiwa rundunar tsaron NATO a kudu maso gabashin kasar Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 11 yayin da da dama suka jikata.

Rahotani daga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP sun bayyana cewar maharin, ya tayar da nakiyar da ke dane a babur dinsa ne, a daidai lokacin da ya zo gab da wasu sojojin Naton da ke sintiri a wata unguwa ta garin Khost da ke yankin Gardez a jiya laraba,harin da kungiyar Alqa'ida ta daukin alhakin kaiwa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu