1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari bam akan rijiyoyin man Sudan ta kudu

March 1, 2012

Sudan ta kudu ta bayyana cewar ƙasar Sudan ta kai hari akan wasu rijiyoyinnta na fetur a kodorfan ta kudu da ke kan iyakar ƙasashen biyu.

New oil platforms are constructed , Saturday, Dec. 17, 2005 near Kotch in southern Sudan.Nothing has changed in the way oil wealth is distributed in Sudan, oil and aid workers say one year after a peace agreement to end a petroleum-fueled civil war in the south of Africa's largest country and one of its poorest despite its new-found riches.(AP Photo/Karel Prinsloo)
Daya daga cikin rijiyoyin mai na kudancin Sudan.Hoto: AP

ƙasar sudan ta kudu ta zargi takwararta kuma maƙobciyarta sudan da harba bama-bamai akan  rijiyoyinta na fetur da ke  kusa da iyakar waɗannan ƙasashen biyu da ke gaba da juna. Ministan watsa labaran Sudan ta kudu Barnaba Marial Benjamin da ya yi Allah wadai da abin da ya kira takalar fada ta sudan, ya ce bama-bamai sun lalata wata cibiya ta samar da ruwan sha ga kasarsa a Kodorfan ta kudu. Dama dai ƙasashen biyu na takaddama game da wannan yanki mai arzikin man fetur. Sudan da kuma sudan ta kudu na zargan junansu da ɗaure wa 'yan tawayen ƙasashen na su gindi da nufin haddasa rikici a cikinsu.

A nata ɓangaren kasar Amirka  ta zargi shugaba Omar Hasan al-Bashir na Sudan da hanna ruwa gudu a ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya tsakanin ƙasarsa da kuma sudan ta kudu. sakatariyar harkokin wajen kasar ta Amirka wato Hilary clinton ta bayyana wa majalisun ƙasarsat cewar shugaban sudan na ƙoƙarin yin kafar  ungulu ga yarjejeniyar sulhun da ƙasarsa ta kulla da Sudan ta Kudu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman