Hari da wuka ya yi sanadin rai a London
August 4, 2016Talla
Mace guda ta rasu yayin da wasu biyar suka sami raunika a wani hari da wuka a dandalin Russell na birnin London. A wani jawabi da jami'an 'yan sanda suka fitar sun bayyana cewa ba za a kebe wannan hari daga cikin irin na 'yan ta'adda ba duk da cewa an gano wanda ya kai shi matashi ne da ke da tabin hankali. Mark Rowley shi ne mataimakin kwamishinan 'yan sanda da suka fita aiki na musamman bayan afkuwar lamarin a birnin na London:
"Matashi dan shekaru 19 an kama shi jim kadan bayan karfe tara da minti 39 yana kuma hannun 'yan sanda, duk da cewa akwai alamun tabin hankali a tattare da shi ba za a cire harin ta'addanci ba. Mutane shida abin ya shafa mace guda ta rasu baya ga wasu matan biyu da maza uku da suka sami raunika."