1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Hari kan dam na barazanar haddasa ambaliyar ruwa a Sudan

Mouhamadou Awal Balarabe
November 18, 2023

Sojojin da ke biyeyya ga gwamnatin Sudan da kuma dakarun sa-kai na RSF sun zargi junansu da kai harin da ya lalata gada ta madatsar ruwan Jebel Awlia da ke kudancin birnin Khartum.

Irin wannan madatsar ruwan Merowe ne ake kai wa hari a kudancin khartum
Irin wannan madatsar ruwan Merowe ne ake kai wa hari a kudancin khartumHoto: picture-alliance/Photoshot

Har yanzu ba a tantance girman barnar da aka yi a madatsar ruwan ba, amma dai tana barazanar haddasa ambaliya ruwa. A baya-bayan nan, fada ya karu a yankin Jebel Awlia wanda ya yi sanadin raba dubban mutane da matsugunansu, a wannan gunduma mai fama da talauci a kudancin lardin Khartum.

A farkon wannan watan ne, dakarun RSF ta mataimakin shugaban kasar Mohammed Hamdan Daglo ta ce ta kama wani sansanin sojoji a yankin. Sannan a cikin 'yan makonnin da suka gabata, an lalata wata gada a babban birnin kasar Khartum tare da lalata wata muhimmiyar ma'ajiyar man fetur a hare-haren da bangarorin biyu ke zargin junansu da kaiwa.