Hari kan jirgin kasa a Najeriya
March 9, 2018Tsoron satar ta mutane ne dai ya kai mafi yawa na masu hannu a cikin shuni mantawa da batun motocin alfarma tare da zabar jirgin kasa mai gudu, a matsayin hanyar zirga-zirga a tsakanin Abuja cibiyar mulkin Tarrayar Najeriya da kuma Kaduna da ke zaman cibiya a Arewa. Tun kafin nan dai an kama da dama a cikinsu tare da karbar miliyoyin Nairori a cikin wani tsarin da ya kalli kara ta’azzara ta satar al’umma a tsakanin manyan biranen guda Biyu. To sai dai kuma daga dukkan alamu shegun suna shirin tare a wajen gari sakamakon wani hari na bindiga kan jirgin da ke kan hanyarsa daga Abuja zuwa kaduna a cikin wannan mako.
Duk da cewar dai jirgin ya yi nasarar isa Kadunan ba tare da rauni ko asara ta rayuwa ko kuma nasarar tsaida shi domin satar ba, ana dai kallon harin a matsayin wani yunkuri a bangare na barayin da ke neman karkatar da sana’ar ta su daga babban titin da ya hada biranen guda biyu, ya zuwa layin dogon na zamani daya tilo a kasar. Abun kuma daga dukkan alamu ke iya kai wa ga bude sabon babi cikin rikicin rashin tsaron da ke rikidewa a sassa daban-daban na Tarrayar Najeriyar.
Nasarar akan matafiya ta jirgin kasa da ake yiwa kallon daya tilo da bashi da wani hatsari daga dillallan a mutun dai na iya dora kasar zuwa wani sabon matsayi ga batun tsaro da zama na lafiyar al’ummarta. Ko a cikin wannan mako dai rundunar 'yan sandan kasar sun nuna wasu matasa 47 da suka ce barayin shanu ne da masu satar mutane da kuma 'yan fashi da makamai da kuma barayin motoci da suka addabi jihohin Nasarawa da Abuja da Kaduna da kuma jihar Niger, duk dai a cikin yankin na Arewa. Abun jira a gani dai na zaman tasiri na harin bisa halin rashin tsaron da ke ta ruruwa irin ta wutar daji a ciki dama wajen yankin Arewacin kasar.