Hari kan masallacin Sunni a Iraki
August 22, 2014Wasu 'yan bindiga sun bude wuta kan masu ibada lokacin sallar juma'a a wani masallacin 'yan Sunni da ke garin Imam Wais a yankin arewa maso gabashin Bagadaza, akalla mutane 32 suka hallaka, a cewar mahukuntan Iraki.
Sai dai an yi ta samun rahotanni mabanbanta dangane da wadanda suka kai harin da ya kai ga jikkatar mutane da dama. Wasu majiyoyin sun dora alhakin harin kan mayakan 'yan Shi'a a yayinda wasu kuma suke dorawa mayakan IS mai da'awar kafa kasa mai bin tafarkin Islama.
Wani mazaunin garin ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa cewa mayakan 'yan Shi'a ne suka kai harin, domin daukar fansar wani harin bam da ya yi musu ta'adin gaske.
Wani Kaftin na soja da wani dan sanda, su kuma sun ce mayakan IS ne inda wani mai kunar bakin wake ya tayar da bam din a cikin masallaci, a yayinda sauran maharan suka rika harbin bindiga kan masui ibadan da suke kokarin tserewa daga masallacin.
Tun a watan Yui ne mayakan IS suka fara jagorantar hare-haren da suka kai ga mamayar larduna biyar. Hari farko da aka kai ya janyo hasarar jami'an tsaron kasar, abin da ya sanya gwamnati neman tallafi daga mayakan 'yan Shi'ar da ta rika yaka na wani tsawon lokaci yanzu.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe