Hari kan sansanin sojin sama a Maiduguri
December 2, 2013Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewacin Najeriya na cewa hukumomin jihar sun sanya dokar hana fita tsawon sa'o'i 24 biyo bayan hari da ake kyautata zaton 'yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ce su ka kai wani sansani na sojin sama a birnin.
Wasu da suka shaida faruwar wannan lamari kuma suka zabi a sakaya sunayensu sun ce maharan sun farwa sansanin ne kafin assalatu inda suka tada bama-bamai da harbe-harbe, inda daga bisani suka ga motocin asibiti na wuce da gawawakin da ke da harbin bindiga yayin da wasu kuma an yi musu yankan rago.
Ganau din sun kuma ce harin ya shafi wasu jiragen sojin saman na Najeriya guda uku da ma dai motoci soji da dama wanda suke kone kurmus.
Wannan harin dai na zuwa ne mako guda bayan da da rundunar sojin saman ta Najeriya ta kai sumame da jiragen yaki a wasu dazuka da ke kan iyaka kasar da Jamhuriyar Kamaru inda ake kyautata zaton 'yan Boko Haram din na boye.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Saleh Umar Saleh