Hari kan soji a Afghanistan
October 2, 2014Talla
Jami'ai sun bayyana cewar wani ɗan kunar baƙin wake da ya tashi kansa a wani harin kunar bakin wake, bayan hallaka kansa ya kuma kashe wasu jami'an soji uku, da raunata wasu bakwai a birnin Kabul kwana daya bayan da aka kai irin waɗannan hare-hare har sau biyu da suka yi sanadin kisan mutane 11. Hafeiz Khan da ke zama shugaban 'yan sanda a lardin ya bayyana cewar ɗan ƙunar bakin waken ɗaure da bama-bamai ya tashi bam ɗin ne a kusa da wata mota kirar bus da ta ɗauko sojoji a safiyar Alhamis ɗin nan kan hanyar su zuwa wurin aiki.