Hari kan yan sanda a Mombasa na Kenya
October 17, 2012Talla
Kakakin rundunar 'yan sandan Kenya,Laftana kanar Aggrey Adoli,ya bayanawa kafofin yada labarai cewar kimanin 'yan sanda goma ne suka samu munayen runika a wani harin guurnetin da aka kaiwa ayarin motocinsu a wannan Larabar. Tun bayan da kasar ta Kenya ta kuduri fattatakar mayakan kungiyar kishin Islama Al-shebab a Somaliya,kasar ke fuskantar hare-haren ta'addanci wadanda mayakan kungiyar ke kamantawa da ramuwar gaya.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Umaru Aliyu