1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jilli: Hari kan 'yan ta'adda ko farar hula?

April 14, 2026

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da masana harkokin tsaro na ci gaba da mahawara kan yawan kai hari kan fararen hula bisa kuskure.

Nigeria Maiduguri 2026 | Soldaten nach tödlichem Selbstmordanschlag
Hoto: Audu Marte/AFP/Getty Images

Muhawara kan karuwar asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon irin wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun samu bayanan sirri tun kafin wannan mummunan hari da ya auku a yankin wanda yayi sanadiyyar mutuwa babban kwamanda a Benisheikh da wasu sojoji amma ba a dauki matakai da suka kamata ba.

Wannan hari da jiragen yaki suka kai kasuwar Jilli da ke kan iyakokin jihohin Borno da Yobe shi ne karo na 13 da ake zargin irin wannan kuskure ya faru, abin da ke kara jefa tambayoyi kan ingancin dabarun soji da kuma hanyoyin tantance bayanan sirri kafin kai hare-hare.

Wasu kungiyoyi kare hakkin bani Adama da suka damu kan yawaitar irin wadannan hare-haren sojojin Najeriya kan fararen hula na ganin duk da cewa sojoji na kokarin yaki da kungiyar Boko Haram, wajibi ne a kara inganta hanyoyin tantance fararen hula da ‘yan ta'adda domin kauce wa asarar rayukan fararen hula.

Hoto: REUTERS

Ambasada Hafzi Aminu Daiba daya daga cikin shugabannin kungiyoyin fararen hula a Najeriya ya ce abun da ya ke faruwa na irin wadannan hare-hareabun tashin hankali ne musamman yadda aka gaza magance su.

Gwamnatin jihar Borno dai ta ce ba ta taba goyon bayan kashe fararen hula ba amma dai wannan kasuwa an rufe ta shekaru biyar da suka shude. Masana tsaro kamar Air Commodore Ahmad Tijjani Baba Gamawa mai ritaya na ganin matukar ana son magance irin wadannan kura-kurai sai al'umma sun taimaka wa jami'an tsaro maimakon ‘yan ta'adda.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun samu bayanan sirri tun kafin wani mummunan hari da ya auku a Benisheik to amma ba a iya daukar matakai da suka kamata ba.

Hoto: Mohamed Tidjani Hassane/DW

"An samu sahihan bayanai na sirri kan cewa wadannan mayakan za su kawo hari zuwa wannan sansanin kwanaki kafin a kawo harin, ban san yaya aka yi har aka kai harin ba tare da an dauki matakai da suka kamata ba. Ko da ya ce wannan ba lokaci na dora alhaki kan wani ba amma ina ganin akwai bukatar sake fasalin tsaro da ake amfani da shi yanzu".

Masana tsaro da al'umma na nuna damuwa kan zargin gazawa wajen amfani da bayanan sirri, lamarin da ke haifar da tambayoyi kan matakan tsaro inda hukumomi ke cewa suna duba lamarin tare da alkawarin gyara a nan gaba

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW