Akasarin yara a yankin masu magana da Turancin Inglishi a Kamaru sun daina zuwa makarantar boko. A shekaru uku na baya bayan nan duk wadanda suka yi karambanin tafiya makarantar sun fuskanci hari daga mayakan 'yan aware wadanda suka yi kira da a kaurace wa duk wasu ma'aikatu na gwamnati a yankin.