1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

'Yan ta'adda sun kashe mutane 15

Suleiman Babayo USU
May 22, 2023

Ana ci gaba da samun hare-hare da ke halaka rayuka a kasar Burkina Faso inda sabon harin tsageru masu dauke da makamai sun halaka kimanin mutane 15.

Burkina Faso | Birnin Wagadugu
Sojojin Burkina FasoHoto: Kilaye Bationo/AP Photo/picture alliance

Kimanin mutane 15 suka halaka galibi makiyaya a yankin gabashin kasra Burkina Faso kamar yadda majiyoyin tsaron kasar suka tabbatar.

A irin wannan hare-haren na 'yan ta'adda aka halaka kimanin mutane 20 ranar Jumma'a ta makon jiya a yankin gabashin kasar. Ita dai kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka tana fama da matsalolin tsaro sakamakon hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi.