1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mutane sun halaka a Burkina Faso

September 21, 2023

Hukumomin tsaro a Burkina Faso sun tabbatar da cewa wasu tagwayen haren-hare ta'addanci a yankin Gabas maso tsakiyar kasar sun yi sanadiyyar halaka mutane.

Burkina Faso Ouagadougou Soldaten der Armee
Hoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Gwamnatin ta Ouagadougou ta kuma yi ikirarin kashe 'yan ta'adda goma sha biyu, a wani martani da sojojinta suka mayar ga 'yan ta'addar bayan hare-haren biyu. Masu ikirarin Jihadi dai sun addabi Burkina Fasoda munanan hare-haren ta'addanci, inda ya zuwa yanzu suka yi sanadin mutuwar fararen hula da sojoji sama da 17,000 a cikin shekaru takwas da suka gabata.

Hukumomi na ci gaba da karfafa matakan samar da tsaro kananan hukumomin da ‘yan gudun hijirar suka koma matsugunansu domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.