SiyasaAfirka
Tsageru sun halaka sojojin Burkina Faso 12
October 4, 2021Talla
Sojojin Burkina Faso 12 suka halaka yayin da wasu biyar suka jikata sakamakaon harin tsageru masu dauke da makamai a yankin arewacin kasar. Majiyoyin tsaron kasar sun tabbatar da cewa an kai harin a wannan Litinin.
Galibin wannan hare-hare da kasar ta Burkina Faso da ke yankin yammacin Afirka ke fuskanta ana dangantawa da tsageru masu kaifin kishin addinin Islama.