SiyasaAfirka
Kara samun hare-hare a Mali
January 24, 2021Talla
Rundunar sojin Mali ta tabbatar da adadin jami'an sojinta da suka mutu a wani tagwayen harin da aka kai a daren jiya sun kai 6 yayin aka ga gawawwakin wasu 30 da ake zargin mayakan jihadi ne.
Harin dai ya auku ne kusa da iyaka da kasar Burkina Faso, kuma tuni aka kwashe sauran dakarun wadanda suka ji rauni.
Ko a watan Satumbar shekarar 2019 an kai wani hari sansanin dakarun da ke zama mafi munin hare-hare da aka kai Mali tun shekarar 2012, inda sojoji 50 suka rasa rayukansu.