1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaOman

Oman: Hari a kan 'yan Shi'a

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 16, 2024

Rahotanni daga Oman na nuni da cewa wasu 'yan Pakistan sun halaka, yayin wani hari da aka kai a Masallacin 'yan Shi'a a Muscat babban birnin kasar.

Oman | Masallaci | Hari
Hari a Masallaci ya halaka mutane tare da jikkata wasu da dama.Hoto: monticello/Zoonar/picture alliance

Mahukuntan kasar ta Oman sun bayyana cewa kimanin mutanen 30 sun jikkata a yayin harin, wanda ke zaman na ban mamaki a 'yar karamar kasar da ke da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, a kan Musulmi mabiya Mazhabar Shi'ar da ke zaman marasa rinjaye a kasar ta Oman.