Mutane 60 sun halaka samakaon hari a Jamhuriyar Nijar
March 17, 2021Talla
Mahukunta a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da kisan wasu 'yan kasar kusan 60 bayan da wani harin 'yan ta'adda da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai kan wasu yan kasuwa.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Abdourahmane Zakaria wanda shi ne ya tabbata da afkuwar lamarin da kuma kididdigar adadin wadanda suka rasa rayukansu a gidan talabijin na kasar, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar ta Nijar.
Yan kasuwar dai sun hadu da ajalinsu ne a lokacin da suke dawo wa daga cin wata kasuwar dabbobi ta Banibangou a yankin Tllaberi da ke makwabataka da kasashen Mali da Burkina Faso.