1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe Musulmi 'yan Shi'a biyu a Portugal

March 28, 2023

Mutum biyu sun bakunci lahira yayin wani hari da aka kai da yuka a wata cibiyar haduwar musulmi mabiya tafarkin shi'a da ke a birnin Lisbon fadar gwamnatin kasar Portugal.

'Yan sandan Portugal a cibiyar haduwar Musulmi ta Lisbon.Hoto: Armando Franca/AP Photo/picture alliance

 

A cewar rundunar 'yan sandan kasar bayan kisan mutane biyu a cibiyar dake zama gurin haduwar musulmi mabiya tafarkin Shi'a maharin ya jikkata wasu mutane da dama kafin jami'anta su bindigeshi a lokaci da suke kokarin kama shi.

Tuni dai firaministan Portugal din Antonio Costa  ya nuna alhini tare da jajanta wa al'umma Musulmi mabiya tafarkin Shi'a da yawansu ya kai mutum dubu dari bakoye (7.000) a kasar, sannan kuma ya kawar da maganar ko harin ya na da alaka da ta'addanci.