1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haribo ya janye alawar Happy Cola a Netherlands

Abdullahi Tanko Bala
May 29, 2025

Kamfanin Alawar Haribo ya janye alawar Happy Cola da ya sayar a Netherlands bayan da aka gano tabar wiwi a cikin kwalin alawar, Mutane da dama ciki har da kananan yara sun sami rashin lafiya a sakamakon haka.

Alawar Haribo
Hoto: MIGUEL MEDINA/AFP

Kamfanin Haribo ya janye alawar Happy Cola da ya sayar a Netherlands bayan da aka gano tabar wiwi a cikin kwalin alawar. Mutane da dama ciki har da kananan yara sun sami rashin lafiya a sakamakon shan alawar.

Hoto: Ulrich Wagner/IMAGO

Hukumar kula da ingancin abinci ta kasar Holland ta ce kwalaye uku ne kawai aka gano suke dauke da tabar ta Wiwi, sai dai an bukaci dawo da dukkan alawowin saboda matakan kariya.

A cikin wata sanarwa mai magana da yawun hukumar kula da ingancin abincin ta Netherlands ta ce shan alawar ka iya haifar da yanayin rashin lafiya kamar Jiri da sauran su.

Hoto: Walter Bieri/dpa/picture alliance

Yan sanda sun sanar da hukumar ingancin ne bayan da mutane da dama da suka hada da kananan yara suka kamu da rashin lafiya bayan da suka sha alawar ta Happy Cola.

Patrick Tax mataimakin shugaban kamfanin alawar Haribo ya ce suna daukar lafiyar masu sayen kayansu da muhimmanci a saboda haka suka janye alawar daga kasuwa tare da bukatar dukkan wadanda suka saya su dawo da ita.