Harin ƙunar baƙin wake a Pakistan ya hallaka mutane 16
September 11, 2007Talla
Wani ɗan ƙunar baƙin wake, a ƙasar Pakistan, ya tarwatsa bam a jikinsa, a yayin da yan sanda ke kore da shi.
A nan take! mutane 16 su ka rasa rayuka, wanda su ka haɗa da jami´an tsaro 3.
Wannan ta´adi ya wakana a birnin Dera Ismail Khan, dake yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Hare- hare, sun ƙara tsamari a ƙasar Pakistan, tun bayan artabon da aka yi, tsakanin ɗaliban jan Massalaci, da dakarun Gwamnatin a birnin Islamabad.
Daga watan juli zuwa yanzu, ɗaruruwan mutane su ka rasa rayuka, a sassa daban-daban na ƙasar a cikin hare-hare daban-daban.