1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ƙunar baƙin wake a Pakistan

June 12, 2011

Aƙalla mutane 34 ne suka mutu sakamakon tashin bam a ƙasar Pakistan

Ma'aikatan ceto a PeshawarHoto: AP

Wasu tagwayen hare-haren bam da aka ƙaddamar a birnin Peshawar na ƙasar Pakistan sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 34, a yayin da wasu da dama kuma suka sami rauni. Fashewar dai ta afku ne a wani yankin dake da wata kasuwar da mutane ke yawaita kai komo a wurin, a birnin da kuma ke yawan fuskantar tashe-tashen hankula a yankin arewa maso yammacin ƙasar ta Pakistan.

Ceton waɗanda suka jikata a harin ƙunar bakin wake a PeshawarHoto: AP

Hakanan kuma ofisoshin gidajen jaridu da dama ne ke kusa da wurin da lamarin ya afku. Jami'an 'yan sanda dai suka ce alamu na nuna cewar 'yan harin ƙunar baƙin wake ne suka ƙaddamar da hare-haren. Sai dai kuma babu wata ƙungiyar da ta ɗauki alhakin ƙaddamar da hare-haren ya zuwa yanzu, amma mayaƙan ƙungiyar Taliban sun sha alwashin ɗaukar fansa game da kisan jagoran al-Qa'idah Osama Bin Laden da dakarun Amirka suka yi a yankin arewa maso yammacin Pakistan a watan jiya.

Sai dai kuma kakakin ƙungiyar Taliban a Pakistan Ehsamunllah Ehsan, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa - ta wayar tarhjo cewar, ba ƙungiyar bace ta ƙaddamar da hare-haren, domin kuwa a cewarsa suna kai farmaki ne akan sojoji da kuma jami'an gwamnati. Ya kuma ƙara da cewar harin, wani munafuncin hukumomin leƙen asirin ƙasashen waje ne dake aikata ta'asar domin shafa musu kashin kaji.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Abdullahi Tanko Bala