Al-Shabaab ta hallaka wani jami'in tsaro
June 22, 2016Talla
Mai tsaron lafiyar Mohammed ne dai ya harbe shi har lahira a garin Jowhar na kasar ta Somaliya. Abdiweli Ibrahim Mohammed dai ya kware matuka a harkar tsaro musamman fannin leken asiri, wanda da taimakon bayanan sirrin da ya ke ba wa jami'an tsaron kasar ta Somaliya ne ma, suka samu nasara a kan 'yan ta'addan na Al-Shabaab a kwanakin baya. Kungiyar ta Al-Shabaab na iko da yankuna masu tarin yawa a Somaliya, kuma ma ta na kiran kanta da kungiyar Al-Qa'ida reshen Gabashin Afirka. A kalla dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar hadin kan Afirka AU 22,000 ne, ke taimakawa gwamnatin kasar Somaliya a yakin da take da kungiyar ta Al-Shabaab.