Sabon harin al-Shabaab a Mogadishu
January 17, 2023Talla
Harin na zuwa ne bayan da gwamnati ta ayyana nasarar kwace wani muhimmin garin bakin ruwa da ke karkashin ikon mayakan.
Akwai rahotanni masu karo da juna dangane da adadin rayuka da suka salwanta a lokacin harin na wannan Talata a garin Hawadley.
Jagoran rundunar sojin Somaliya Odowaa Yusuf Rage, ya sanar a kafar yada labaran Somaliyan cewar sojoji biyar ne suka mutu, a harin da al-Shabaab ta dauki alhakin kai wa. A daya hannun kuma wani shugaban haula a yankin ya ce an kashe jami'an soji 11.