Harin Amirka a Pakistan
June 8, 2013Firaministan Pakistan Nawaz Sharif ya aikewa da jakadan Amirka a kasar sammaci na ya bayyana gabansa domin yi masa bayani game da wani hari da jirgin Amirka da bai da matuki ya kai wani yanki na kasar wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane tara.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewar harin ya wakana ne a yankin arewacin Waziristan da ke kan iyakar Pakistan din da Afghanistan cikin dare jiya Juma'a, lamarin da sabbin mahukuntan kasar su ka ce abu ne da ba za su lamunta ba.
Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Pakistan din ta sabunta kiran da a baya ta yi wa Amurka na ta daina kai hare-hare da jiragen da ba su da matuka wanda ta ce hakan keta alfarmar kasarta ce.
Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki goma bayan da wani makamancinsa ya yi sanadiyyar rasuwar mataimakin shugaban kungiyar nan ta Taliban Waliyu Rahman da wasu mukarabbansa shidda.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman