1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Harin Amurka a Somalia ya hallaka mayakan ISIS

Binta Aliyu Zurmi
February 2, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin kaddamar da hare-hare ta sama kan mayakan ISIS a tsaunin Golis na kasar Somalia.

US Luftschlag gegen IS-Terroristen in Somalia
Hoto: U.S. Africa Command/AP/dpa/picture alliance

Shugaba Trump wanda ya ce an kashe wasu manyan mayakan da kuma lalata maboyarsu, ya kara da cewar Amurka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen murkushe duk wata kungiya da ke zama barazana a garesu.

Duk da cewar mayakan ISIS a kasar ta Somalia ba su da yawa kamar mayakan al-Qaeda, sai dai suna daga cikin manyan kungiyoyi masu ikirarin jihadi da suka bulla tun a shekarar 2010.

A baya Amurka ta sha kaddamar da hare-hare a Somalia, musamman a shekarar da ta gabata da nufin kawo karshen ayyukan mayakan masu ikirarin jihadi.

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohammed ya mika sakon godiya ga Washington biyo bayan harin da ya ce a ci gaba da kai irin sa zai taimaka wajen fatattakar mayakan daga kasarsa.
 

Karin Bayani:Sojojin Somaliya sun murkushe 'yan bindiga